Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Juyin Musulunci na Iran a ranar Alhamis 9 ga Yuli a cikin wata sanarwa sun rubuta: A sanarwar da ta gabata mun ce maimaita ta'addanci zai faɗaɗa martaninmu ga sauran sansanonin makiya a yankin, kuma a mataki na biyu na martani ga ta'addancin sojojin Amurka masu kashe yara, mun aiwatar da wannan barazana.
A ci gaban wannan sanarwa yazo cewa: Mayakan sararin samaniya na dakarun juyin musulunci da karfe 2:20 na yammacin yau, sun murkushe cibiyar kwamandanci da sarrafawar makiya a Yammacin Asiya da sansanin sojan saman makiya a Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na ballastic guda 10.
Dakarun Juyin Musulunci a cikin sanarwarsu sun jaddada cewa: Idan aka maimaita ta'addancin sojojin ta'adda na Amurka, sauran sansanonin Amurka a yankin ba za su tsira daga wutar mu mai tsanani ba.
......................
Your Comment